in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya baiwa wadanda bala'in zaftarewar laka ya shafa a Saliyo taimakon gaggauwa na dala miliyan 13
2017-08-30 09:16:15 cri

Jami'in bankin duniya dake kasar Saliyo Parminder Brar ya sanar da cewa, bankin ya samar da taimakon dala miliyan 13 ga wadanda iftila'in zaftarewar laka ya shafa a kasar Saliyo, bala'in da ya halaka rayukan daruruwan mutane a birnin Freetown baya ga wasu dubban jama'a da suka rasa matsugunansu.

Mr Brar wanda ya sanar da wannan tallafi yayin taron manema labarai da aka shirya a babban ofishin bankin dake birnin Freetown, fadar mulkin kasar ta Saliyo, Ya kuma ce, a farkon wannan watan, ma'aikatar kudi da raya tattalin arziki ta kasar ta tuntubi bankin game da neman taimakon kudi don tunkarar wannan matsala, da bukatar daukar matakan gaggauwa kan bala'in da kuma kimanta irin barnar da ta haddasa, ta yadda za a samu saukin aiwatar da matakan taimakawa wadanda lamarin ya shafa, da kuma gyara wuraren da suka lalace.

Ya bayyana cewa, yanzu haka bankin ya tura tawagar kwararru a fannin kula da bala'u zuwa birnin Freetown inda za ta yi aiki fadada da kafada da gwamnati, hukumomin MDD da na cikin gida, don kimanta abubuwa da ake bukata na gaggauwa a gajere da kuma matsakaicin lokaci.

Jami'in bankin duniyar ya kuma ce, bankin yana tantance barnar da bala'in ya haddasa a cikin biranen kasar uku, wato Freetown, da Makeni, da kuma Bo. Inda yake fatan hada rahotonsa a cikin watan Nuwamban wannan shekara don mika shi ga shugaban kasar ta Saliyo. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China