in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Sin sun ayyana matakin gaggawa a lardin Guizhou
2017-08-28 20:41:07 cri
Mahukuntan kasar Sin sun ayyana matakin gudanar da ayyukan gaggawa mai lamba IV a yau din nan, ga yankin Zhangjiawan dake garin Bijie na lardin Guizhou inda aka samu zabtarewar kasa.

Tuni sashen dake lura da ayyukan dakile annoba na ma'aikatar kula da lamurran al'umma, ya aike da jami'ai domin gudanar da ayyukan ceto, da na samar da sassauci ga wadanda ibtila'in ya shafa.

Zaftarewar kasar da ta auku da misalin 11 saura minti 20 na safiyar yau litinin, inda ta shafi iyalai 34. An kuma tabbatar da rasuwar mutane 2, yayin da kuma ake ci gaba da neman wasu mutanen 25 da suka bace. Kaza lika mahukunta sun samar da tallafin tantuna, da shimfidu domin amfanin wadanda aka tsugunar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China