Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya auku ne da sanyin safiyar yau Litinin da misalin karfe 11 saura minti 20, kuma ya shafi iyalai 34, tuni kuma aka fara ayyukan ceton rayuwan wadanda suka bace.
Ma'aikata dai sun riga sun gano gawawwakin mutane biyu, sun kuma cewo wasu mutanen 4 da lamarin ya rutsa da su, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutane 25 da suka bace. A hannu guda mahukuntan dake lura da bala'u, sun riga sun samar da kayan tallafi da suka hada da tantuna, da shimfidu, domin amfanin wadanda aka tsugunar.