in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi da Tillerson sun zanta ta wayar tarho
2017-08-24 11:36:26 cri
Dan majalissar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, da sakataren wajen Amurka Rex Tillerson, sun zanta ta wayar tarho, game da batutuwan da suka shafi alakar sassan biyu, da kuma batun kasar Afghanistan.

Da yake tsokacin yayin zantawar a jiya Laraba, Mr. Yang ya bayyana cewa, Sin da Amurka na ci gaba da bunkasa hadin gwiwa da juna a fannoni da dama, musamman bangarorin da za su zamo masu alfanu gare su, da ma sauran kasashen duniya baki daya.

Ya ce bisa kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, kasashen Sin da Amurka, na da burin fadada musaya a matakin jagoranci, da ma na hukumomi, tare da ci gaba da shirye shiryen ziyarar da shugaba Trump zai gudanar a Sin nan gaba cikin wannan shekara, bisa gayyatar shugaba Xi.

Mr. Yang ya kara da cewa, yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da bunkasa hadin gwiwarsu, tare da warware banbancin ra'ayi ta hanya mafi dacewa, kana su cigaba da raya dangantakar su yadda ya kamata.

A nasa bangare kuwa, Mr. Tillerson cewa ya yi, Amurka na fatan aiki tare da Sin wajen aiwatar da yarjeniyoyin da shugabannin sassan biyu suka cimma, tare da karfafa tattaunawa.

Mr. Tillerson ya ce shugaba Trump na maida hankali ga ziyarar sa a Sin, don haka ya yi fatan kammalar dukkanin shirye shirye da suka wajaba domin cimma nasarar hakan.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China