in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana samun bunkasuwa a sha'anin mutum-mutumin inji
2017-08-24 11:34:39 cri

Wani rahoto da sashen tattara bayanai na Bloomberg Intelligence ya fitar a wannan mako ya nuna cewa, kasar Sin ta sayi mutum-mutumin inji dubu 90 a shekarar 2016, adadin da ya kai daya bisa uku na jimillar yawan mutum-mutumin inji na duniya baki daya, kuma wannan sauyi da aka samu a fannin mutum-mutumin zai iya kara daga matsayin gogayya a sha'anin tattalin arzikin kasar Sin.

Yin amfani da mutum-mutumi a masana'antun kasar Sin yana sake karuwa, inda a halin yanzu kasar ta yi amfani da 1 bisa 3 na yawan mutum-mutumi na duniya baki daya a shekarar 2016, kuma ana saran adadin zai iya ninkawa biyu zuwa dubu 160 a shekarar 2019, kamar yadda alkaluman kididdigar hukumar kula da mutum-mutumin inji ta kasa da kasa ta fitar.

Sakamakon yawan adadin ma'aikatan kasarta, har yanzu kasar Sin tana sahun baya idan aka yi la'akari da adadin mutum-mutumi a kasar. Akwai kimanin mutun-mutumi 50 a tsakanin ma'aikata dubu 10 a kasar, idan an kwatanta da 75 mafi karanci bisa tsarin kasa da kasa.

Albashin ma'aikatan kamfanonin cikin gida wadanda ke da shaidar karatu mai zurfi, ya karu da kashi 53 cikin 100 daga shekarar 2010 zuwa 2014, inji wata kididdigar da kasar Sin ta fitar game da sha'anin tattalin arziki na magidanta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China