Kakakin rundunar sojin kasar Ahmad al-Mesmari, ya ce mayakan sun kai hari ne kofar Al-Fagha dake yankin Al-Jufra da safiyar jiya Laraba, inda suka yi wa sojoji 9 da fararen hula 2 yankan rago.
Shingen binciken na da nisan kilomita 500 daga kudancin birnin Tripoli.
Sojoji karkashin Janar Khalifa Haftar, sun shafe sama da shekaru 3 suna yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a gabashin Libya.
A farkon watan Yuli ne rundunar sojin ta sanar da kwace iko da garin Benghazi, birni mafi girma na biyu a Libya.
A kuma Cikin watan Decemban bara ne, dakarun da hadin gwiwar gwamnatin hadin kan kasar da MDD ke marawa baya, suka 'yanto Sirte, birnin dake da nisan kilomita 450 daga gabashin Tripoli, bayan shafe kusan watanni 7 suna gwabza fada da mayakan IS.
Sai dai, duk da wadannan nasarori da aka samu, har yanzu akwai ragowar mayakan IS a wasu sassan Libya. (Fa'iza Mustapha)