in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Nijeriya za ta kakkabe yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba a jihar Enugu
2017-08-23 12:37:22 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce za ta kakkabe makamai ba bisa ka'ida ba a jihar Enugu dake kudu maso gabashin kasar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Enugu Danmallam Mohammed, ya ce ana samun yawaitar muggan makamai a hannun matasa har ma da manya a jihar.

Danmallam Mohammed wanda ya bayyana haka yayin taron yini daya kan tsaro da ya gudana tare da masu ruwa da tsaki, ya ce wannan mummunan al'amari ya haddasa tashe-tashen hankula da suka kai ga asarar rayukan 'yan Nijeriya maza da mata.

Ya shaidawa mahalarta taron cewa, 'yan sanda na gudanar da bincike kan zargin wasu munanan dabi'u da wasu kungiyoyi ke yi, da suka hada satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da fyade da kisa da sauransu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China