in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan Sin ya isa Namibia domin ziyarar aiki
2017-08-23 11:09:20 cri

Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli ya sauka kasar Namibia, domin ziyarar aiki, wadda ke da nufin bunkasa dadaddiyar alaka, da kawance dake tsakanin Sin da kasar Namibia.

Da yake tabbatar da hakan yayin wani taron 'yan jaridu da ya gudana a birnin Windhoek, jakadan kasar Sin dake Namibia Zhang Yiming, ya ce Mr. Zhang Gaoli zai kasance a Namibia tsakanin ranekun 26 zuwa 29 ga watan nan na Agusta.

Jakada Zhang, ya ce Sin da Namibia na fatan ci gaba da bunkasa hadin gwiwa a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da ilimin kimiyya, da kuma fannin raya al'adu.

Baya ga zantawa da shugaban kasar ta Namibia Hage Geingob, mataimakin firaministan na Sin zai kuma ziyarci wuraren da ake gudanar da ayyukan ci gaban sassan biyu, kamar mahakar makamashin Uranium dake Husab, da sashen sauke hajoji na Walvis Bay, da aikin kafa na'urar tattara bayanai ta tauraron dan adam, da dai sauran su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China