in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Kano yana fatan Sin da Najeriya za su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu
2017-08-22 10:41:10 cri

A kwanakin da suka gabata ne mai martaba sarkin Kano dake tarayyar Najeriya Muhammadu Sanusi II da tawagar sa suka ziyarci wasu birane na kasar Sin, bisa gayyatar da kungiyar sada zumunta ga kasashen waje ta kasar Sin ta yi musu. Yayin ziyarar ta su, sassan biyu sun yi musanyar ra'ayoyi kan batutuwa game da yadda za a kara karfafa cudanya dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu, da kuma hadin gwiwa da zuba jari da sauransu.

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarimar tattalin arziki, da bude kofa ga kasashen waje, a saboda haka yana fatan kamfanonin kasar Sin za su kara zuba jari a kasarsa, yana kuma sa ran cewa, kasashen biyu wato Sin da Najeriya za su ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, musamman ma a fannonin gina yankunan ciniki marasa shinge, da zuba jari, da sarrafa kayan sawa.

Sarkin mai shekaru 56 da haihuwa, shahararren shugaban gargajiya ne a tarayyar Najeriya, ya kuma taba zama shugaban babban bankin Najeriya tsakanin shekarar 2009 da 2014, kuma mahaifinsa ya taba kasancewa jadakan Najeriya na farko a kasar Sin, tun bayan da Sin da Najeriya suka maido da huldar diplomasiyya tsakaninsu a shekarar 1971.

Sarkin wanda ya jagoranci bankin Najeriya a baya ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da talatin da suka gabata, yana mai da hankali kan manufar yin kwaskwarimar tattalin arziki, da bude kofa ga kasashen waje wadda gwamnatin kasar Sin ta aiwatar, amma a wancan lokaci, ana nuna shakku kan manufar.

Bayan da sarkin da tawagar sa sun kammala ziyara a wasu biranen kasar Sin, musamman ma bayan da suka ganewa idanun su nune-nunen sakamakon da aka samu, tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarimar tattalin arziki da bude kofa ga kasashen waje a birnin Shenzhen, sun nuna gamsuwa da amincewarsu ga matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka domin raya kasa, saboda wadannan matakai sun dace da hakikanin yanayin da kasar ke ciki. Sarkin yana mai cewa, "Ina ganin cewa, idan shugaban kasa yana da hangen nesa, kuma ya nace ga kokarin da yake, to ko shakka babu wannan kasa za ta samu ci gaba. Birnin Shenzhen ya ba da misali ga sauran biranen kasar wajen bude kofa, ya taka muhimmiyar rawa wajen raya kasa. Ina da tunanin cewa, me ya sa Najeriya ba ta yi koyi da kasar Sin ba? Ina tsammanin, mu ma muna iya zabar wasu birane domin fara aiwatar da munufar bude kofa, misali a jihar Lagos."

Sarki Muhammad Sanusi II ya amince cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, wasu kasashen Afirka kamar su Habasha da Sudan da Afirka ta Kudu, sun samu jarin kasar Sin mai tarin yawa, ta hanyar kyautata muhallansu na zuba jari da kasuwanci, ta haka sun samu babban sakamako wajen raya tattalin arzikinsu. Yanzu haka ya zama wajibi Najeriya ta kara kyautata manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, musamman ma a fannin samar da lantarki, ta yadda za ta kara samun jarin da kamfanonin kasar Sin za su zuba a nan gaba.

Kana sarkin ya nuna fatan cewa, kamata ya yi Najeriya ta koyi fasahohin kasar Sin wajen gina yankin ciniki maras shinge, yana mai cewa, "Wasu biranen Najeriya, misali Lagos, su ma suna bakin teku kamar birnin Shenzhen, shi yasa muke fatan za a gina yankunan ciniki marasa shinge a wuraren, kamar yadda ake yi a Shenzhen, da haka birnin Lagos zai samu bunkasuwa har ya kai cibiyar tattalin arziki ta duniya."

A baya sana'ar kayan sawa masana'antun gargajiya ne a Najeriya ke gudanar da ita, inda masu aikin samar da kayan sawa a wannan fanni suka taba zarta dubu 700, amma yanzu aikin ya gamu da kalubale da koma baya. Yayin ziyararsa a birnin Shanghai, sarkin ya ziyarci kamfanin samar da kayan sawa na Shanghai, domin tattaunawa kan hadin gwiwa da kasar Sin a fannin raya masaku. Sarkin ya bayyana cewa, kasar Sin tana da fasahohin sana'ar da Najeriya take bukata, saboda haka yana fatan kamfanin sawan kasar Sin za su shiga jihar Kano, wadda ke kan gaba wajen ci gaban kasuwanci a kasar, domin gina kamfanin samar da kayan sawa, ya ce, "Mun zo kasar Sin ba domin samun rancen kudi ne kawai ba, muna fatan kara samun jarin da kasar Sin za ta zuba domin raya tattalin arzikin kasarmu. Ban da haka kuma, yayin da masu zuba jari na kasar Sin suka zo kasarmu, dole ne mu samar musu moriyar da suke bukata."

Sarki Sanusi II ya jaddada cewa, yana maraba ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Najeriya, kuma gwamnatin Najeriya ita ma za ta yi iyakacin kokarin ta, wajen samar da hidima mai inganci a gare su. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China