Zhang Gaoli, zai isa birnin Khartoum a ranar Juma'a domin ziyarar yini biyu bisa gayyatar da mataimakin shugaban kasar na farko kuma Firaministan kasar Bakri Hassan Saleh ya yi masa.
Sanarwar da ministan harkokin wajen ya fitar, ta ce wannan muhimmin ziyara da babban jami'in kasar Sin zai kai, zai inganta huldar dake tsakanin Sudan da Sin tare da jadadda karfin dangantakarsu wanda ke samun tagomashi ta fuskar hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakaninsu.
Zhang Gaoli ya isa Kuwait a jiya Litinin, domin fara ziyarar da yake zuwa kasashe 4, wanda zai kai shi Saudiyya da Sudan da kuma Namibia. (Fa'iza Msutapha)