in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya murnar taron bayar da rahoto game da yadda Sin ke tabbatar da ajantar samun dauwamamman ci gaba kafin 2030
2017-08-21 14:39:44 cri
Yau ranar Litinin a nan birnin Beijing, aka shirya bikin soma aikin cibiyar ilmin ci gaban duniya ta kasar Sin, da kuma taron bayar da rahoto game da ci gaban da Sin ta samu, wajen tabbatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba kafin shekarar 2030. Shugaban kasar Xi Jinping ya aika da wasika don taya murnar bude taron.

A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, kasarsa na dora muhimmanci kwarai kan wannan ajandar, kana za ta dage wajen tabbatar da hakan. Ban da wannan kuma, ya jaddada cewa, cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen yin cudanyar ra'ayoyin samun ci gaba, da karfafa hadin kai tsakanin kasa da kasa, da kuma inganta tabbatar da ajandar samun dauwamamman ci gaban duniya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China