in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a ibtila'in zaftarewar laka a Saliyo ya kai 499
2017-08-21 13:37:04 cri

Ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, an tsinci gawarwakin mutane da yawansu ya kai 499, a ibtila'in ambaliyar ruwa da zaftarewar laka a ranar 14 ga watan nan na Augasta a kasar Saliyo, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

An samu zaftarewar lakar ne bayan mamakon ruwan sama da aka samu da safiyar ranar 14 ga watan Augasta, inda ya hallaka mazauna yankin, kana ya raba makwabtan inda lamarin ya auku da matsugunansu a wajen birnin Freetown, babban birnin kasar Saliyo, kuma sama da mutane 2,000 ne suka rasa gidajensu.

Shugaban kasar Salyo Ernest Bai Koroma, a ranar Talatar makon jiya, ya ayyana zaman makoki na kwanaki 7 a duk fadin kasar.

Tuni dai kasashen duniya suka fara kai kayan agajin gaggawa zuwa kasar ta Saliyo, kasar Sin da Ghana na daga cikin kasashen da suka fara kai agajin don agazawa mutanen da bala'in ya shafa.

A cewar ofishin jakadancin kasar Sin dake Saliyo, baya ga kayan tallafi da wasu kungiyoyi da kamfanonin kasar Sin dake aiki a Saliyo suka bayar, gwamnatin Sin ta yanke shawarar samar da kayayyakin bada taimakon gaggawa na dalar Amurka miliyan guda ga gwamnatin kasar Saliyo.

Kasar Ghana ta samar da kayan tallafi da darajarsu ta kai dala miliyan daya don agazawa mutanen da ibtila'in ya shafa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China