in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin samun wadata a fadin duniya a taron Durban a 2013
2017-08-21 13:32:03 cri

An gudanar da ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS karo na biyar a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2013, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, abu ne mai muhimmanci a yi kokari tare domin samun wadata a duk fadin duniya. Kawo yanzu shekaru hudu suka gabata, ko wane irin sakamako aka samu a fannin ?

Birnin Durban yana jihar KwaZulu-Natal dake kasar ta Afirka ta Kudu, shi ma babban birni na uku ne a kasar, a shekarar 2013, Afirka ta Kudu ta shirya taron shugabnnin kasashen BRICS karo na biyar a nan, har yanzu ana iya ganin alamar taron a birnin.

Scott Langley yana kula da aikin kasuwa da sayayya a cibiyar taron kasa da kasa ta birnin Durban, a ganinsa, dalilin da ya sa a zabi cibiyar taron da yake aiki wurin shirya taron shugabannin kasashen BRICS shi ne domin kwarewarsa da hidima mai inganci da yake samarwa, yana mai cewa, "Cibiyar taron kasa da kasa ta Durban, ita ce cibiyar taron kasa da kasa ta farko a kasar ta Afirka ta Kudu, kana muna da kwarewa matuka a fannin shirya taron kasa da kasa, ban da haka kuma, muna iya samar da hidima mai inganci ga mahalarta taron. Misali muna iya sauya wurin taro bisa bukatun masu shirya taro, kazalika, matakan tabbatar da tsaron da muke dauka su ma suna da inganci kwarai, hakan na da muhimmanci matuka ga shugabannin kasashen da suke halartar taron. Ina ganin cewa, duk wadannan sun kasance dalilan da ya sa aka zabi cibiyarmu domin gudanar da taron na kasa da kasa."

Hakika, Langley ya yi alfahari kan aikin hidima na cibiyar taron kasa da kasa ta Durban sosai, ban da ganawar shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a shekarar 2013, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, cibiyar taron kasa da kasa ta Durban ita ma ta shirya wasu taruka na kasashen BRICS, Langley ya gaya mana cewa, "Tawagogin wakilan kasar Sin guda biyu sun ziyarci cibiyar taron kasa da kasa ta Durban a shekarar bara, kafin shekaru biyu da suka gabata kuma, kawancen yaki da maganin kara kuzarin 'yan wasa na kasar Rasha ya yi taro a nan, bana ma mun dauki bakuncin shirya dandalin raya tattalin arzikin kudancin Indiya, ina ganin cewa, mai yiwuwa a ki zabar Durban domin shirya taron kasa da kasa, amma tun bayan da aka gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS cikin nasara da kuma kwanciyar hankali, a kara amincewa da aikin hidima na cibiyar taron ta wannan birni na Durban."

Taron shugabannin kasashen BRICS karo na biyar da aka gudanar a shekarar 2013, shi ma shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci irin sa. Yayin taron, shugaba Xi ya gabatar da wani jawabi mai taken "Kara karfafa hadin gwiwa domin samun ci gaba tare", inda ya bayyana cewa, shimfida zaman lafiya da samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa domin samun wadata a duk fadin duniya fatanmu da kuma hakkinmu ne. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashen BRICS, ta yadda za a kara samar da moriya ga al'ummomin kasashen duniya baki daya.

Dan jaridar "Afircan Times" dake kasar Afirka ta Kudu Sun Xianglu ya taba ganin shugaba Xi da idonsa yayin taron da aka yi a Durban a shekarar 2013, yana mai cewa, "Shugaba Xi ya rika murmushi yayin da yake ganawa da manema labarai, ina ganin cewa, ya yi matukar samun karbuwa a wajenmu, kana abu mafi muhimmanci shi ne jawabinsa, wanda yake da babbar ma'ana, tabbas shi shugaba ne na babbar kasa wadda ke taka muhimmiyar rawa a duniya."

Sheihun malamin cibiyar nazarin huldar dake tsakanin kasa da kasa ta Afirka ta Kudu Francis Kornegay shi ma ya amince da ra'ayin shugaba Xi game da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa domin samun wadata tare a duk fadin duniya, yana mai cewa, "A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin samun wadata, ni ma na amince da haka, nan gaba ya fi kyau a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da sauran kasashen duniya, ta yadda za a cimma burin samun wadata a dukkanin fadin duniya."

Darektan cibiyar nazarin kasashen BRICS, ta kwamitin nazarin al'adu da kimiyya na Afirka ta Kudu Jaya Josie yana ganin cewa, ganawar dake tsakanin shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a shekarar 2013 ta samar da wata dama ga shugaba Xi da ya kara gano muhimmancin kasashen Afirka, hakan ya aza harsashe ga hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China