Ma'aikatan ceto sun ce, an garzaya da wadanda suka ji rauni wani asibiti dake birnin Damascus, ciki hadda mutane da dama, wadanda suka ji munanan raunuka.
An dai gudanar da bikin baje-kolin kasa da kasa karo na 59 a ranar 17 a ga watan nan a cibiyar baje-kolin kayayyaki ta Damascus, inda kamfanoni sama da 1600 daga kasashe 43 suka halarta, kana za'a kammala shi a ranar 26 ga wata. Ta hanyar gudanar da irin wannan biki, gwamnatin Siriya na fatan aikewa da wani sako na farfado da tattalin arzikin kasa, da bayyana aniyarta ta yaki da ayyukan ta'addanci.
Tun barkewar rikicin Siriya, dakarun da ba sa ga-maciji da gwamnati, sun rika harba boma-bomai, da rokoki daga karkara zuwa cikin birane, al'amuran da suka janyo hasarar rayukan mutane da dukiyoyi masu tarin yawa.
Tun farkon watan da muke ciki ne, sojojin gwamnatin Siriya ke kara kokarin da suke yi na fatattakar dakarun 'yan hamayya dake gabashin birnin na Damascus. (Murtala Zhang)