Cikin sanarwar da ya fitar, an ce, MDD tana goyon bayan kasar Finland wajen yaki da ta'addanci da masu aiwatar da laifukan tashe-tashen hankula. Mr. Guterres, ya aike da sakon nuna alhini ga gwamnati da kuma al'ummomin kasar Finland, ya kuma yi fatan cewa samun waraka cikin hanzari ga mutane da suka samu raunuka a sanadiyyar harin.
A yammacin ranar 18 ga wata ne, aka kaddamar da harin ta hanyar amfani da wukake a cibiyar birnin Turku, lamarin da ya haddasa rasuwar mutum guda, yayin da mutane 8 suka jikkata.
Rundunar 'yan sandan kasar Finland tana gudanar da bincike kan lamarin wanda ke da nasaba da harin ta'addanci, kuma ta kama mahari guda a birnin Turku a ranar 18 ga wata, sa'an nan, ta kama mutane hudu da ake zargin suna da hannu a harin, yayin da ake ci gaba da neman mutum guda daban. (Maryam)