Shugaban ofishin 'yan sandan na yankin Catalonia mai cin gashin kansa ya bayyana cewa, wata kungiyar ta'addanci dake kunshe da mambobi guda 12 ne ta kaddamar da hare-haren ta'addancin biyu, an riga an kashe mutane 5 daga cikinsu, yayin da aka kama mutane 4 'yan wannan kungiya, kuma an tabbatar da asalin wadanda mutane da ba'a kama su ba a halin yanzu. Mai iyuwa ne, mutane 2 daga cikin wadannan ba a kama su ba sun riga sun rasa rayukansu sakamakon fashewar boma-bomai a wani gini na garin Alcanar dake kusa da birnin Bacerona. (Maryam)