Wani dan kungiyar al'umma Mugisa Mbogemu, ya ce zaftarewar lakar ta auku ne a kauyen Tora dake kusa da tafkin Albert, bayan mamakon ruwan sama da aka shafe ana yi da daren ranar.
Mugisa Mbogemu dake kauyen Tchomia wanda ke makotaka da inda iftil'in ya auku, ya ce yanzu haka lakar ta binne kauyen, kuma ana kokarin ceto mutane.
A cewar wani likita dake yankin Tchomia, kawo yanzu daruruwan mutane ne ke binne karkashin lakar, yayin da aka garzaya da wasu da aka ceto ciki har da mata da yara zuwa asibiti mafi kusa .
Kauyen da iftila'in ya auku na kusa ne da tafkin Albert.
Ana ta samun rahotannin zaftarewar laka a wasu kauyuka, galibi wadanda ke tsakanin tabkuna ko tsaunuka. (Fa'iza Mustapha)