in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jaddada muhimmancin tattunawa game da batun zirin Koriya
2017-08-17 19:55:49 cri

Mataimakin shugaban kwamitin hukumar gudanarwa ta ayyukan soji na kasar Sin Fan Changlong, ya bayyana hawa teburin shawarwari, a matsayin hanya daya tilo ta warware ja in ja da ake ta yi game da batun zirin koriya.

Fan Changlong, ya yi wannan tsokaci ne yayin ganawar sa da babban shugaban rundunonin sojojin Amurka Janar Joseph Dunford. Mr. Fan ya kuma yi kira ga Amurka da ta yi aiki tare da kasar Sin, domin kaiwa ga warware matsalar zirin na Koriya cikin ruwan sanyi.

Ya ce bangaren Sin na da burin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, domin aiwatar da dukkanin matakan da suka dace, tare da kara bunkasa hadin kai da Amurka ta fannin ayyukan soji.

A nasa bangare Janar Dunford ya bukaci sassan biyu da su karfafa musaya a tsakanin su, su kuma rage wagegen gibin dake tsakanin su na fahimta, tare da kaucewa sabani, domin samar da daidaito da ci gaba mai dorewa a ayyukan soji.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China