in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fursunoni 37 sun mutu sakamakon wani bore da ya barke a gidan yari a kudancin Venezuala
2017-08-17 11:18:40 cri
Rahotanni daga kasar Venezula na cewa, kimanin fursunoni 37 ne suka mutu sakamakon wani bore da ya barke a wani gidan kaso a jihar Amazons dake kudancin kasar, kamar yadda babban mai gabatar da kara na kasar ya wallafa a shafinsa na yanar gizo.

Jami'an kasar na cewa, fursunonin sun mutu ne sakamakon arangamar da ta kaure tsakanin fursunoni da jami'an 'yan sanda, lamarin da ya yi sanadin jikkatar jami'an gidan yarin 14.

Mahukunta dai na gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar tashin hankalin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China