Abdulai Bayraytay, wanda kuma shi ne babban jami'in aikin tunkarar annoba a Saliyo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sun samar da wajen zama na wucin gadi ga wadanda suka rasa muhallansu a makarantu daban-daban dake birnin, kuma a yanzu haka, suna samar da busassashen abinci ga mutanen, sai dai duk da haka suna bukatar kari.
Ya kara da cewa yayin da ake bukatar wadancan abubuwa, har yanzu ana ci gaba da aikin gano wadanda ake tsammanin lakar ta binne su.
Jami'in ya ce gwamnati ta damu game da yuwar barkewar cutar amai da gudawa bayan annobar, a don haka take tsananin bukatar magunguna.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar da aka fitar ranar Talata, ta ce mata 83 da maza 105 da kuma yara 109 ne suka mutu sanadiyyar annobar. Sannan yayin da ake ci gaba da aikin ceto, mai yuwa ne a samu karin gawarwaki.
Sanarwar ta ce ana kai gawawwakin ne asibitin Connaught dake birnin Freetown. (Fa'iza Mustapha)