Da yake jawabi yayin bikin mika kayayyakin, jami'in diflomasiyar kasar Sin dake kasar ta Saliyo Wang Xinmin, ya bayyana cewa, al'ummar kasar Sin suna tare da takwarorinsu na Saliyo a wannan lokaci na bakin ciki, kasancewar kasashen biyu tamkar Danjuma ne da Danjummai.
Ya ce yanzu haka, gwamnatin kasar Sin tana kokarin turo da nata tallafin, ta yadda gwamnatin Saliyo za ta taimakawa wadanda wannan bala'in ya shafa.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban kasar Saliyo Victor Bockarie Foh, ya yaba da wannan taimako na kamfanonin kasar Sin dake zauna a kasar ta Saliyo. Ya kuma ba da tabbacin cewa, za a yi amfani da kudade da kayayyakin da aka samar ta hanyar da ta dace.
Ya kuma bayyana matakan da gwamnatin Saliyon ke dauka na ganin an kwashe wadanda ke zaune a yankunan da ake fuskantar barazanar ambaliyar zuwa yankuna marasa hadari, tare kuma da gina musu gidaje masu saukin kudi.
Iftila'in na ranar Litinin da ya rutsa da wajen birnin Freetown, babban birnin kasar, ya binne daruruwan mutane a unguwanni da dama, ciki har da Regent, tsaunin Sugar-Loaf, Kamayama, Kaningo da Dworzark da sauransu.
Wannan dai shi ne bala'in mafi muni da ya taba aukuwa a kasar a tarihinta, inda bayanai ke nuna cewa, dubban mutane sun rasa matsugunansu a sassan birnin Freetown. (Ibrahim Yaya)