in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Saliyo ya sanar da fara zaman makoki na mako guda
2017-08-16 11:17:32 cri

Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma, ya sanar da fara zaman makoki na mako guda a dukkanin fadin kasarsa, domin alhinin rasuwar kimanin mutane 300, wadanda bala'in zaftarewar laka da ambaliyar ruwa suka hallaka.

Cikin wata sanarwar da ya karanta jiya ta kafar talabijin din kasar, shugaba Koroma, ya ce za a yi zaman makokin ne tsakanin ranekun Larabar nan 16 ga wata, zuwa 22 ga watan nan na Agusta, inda za a sassauto tutar kasar kasa kasa. Kaza kila ya umarci 'yan kasar da su yi shiru na minti guda, da karfe 12 na tsakar daren yau Laraba, domin girmamawa ga mamatan.

Bugu da kari shugaban na Saliyo, ya umarci dakarun sojin kasar da su ci gaba da baiwa fararen hula da wannan ibtila'i ya shafa tallafi, yayin da kuma ake fatan wadanda 'yan uwansu suka bace, za su rika zuwa dakin adana gawawwaki dake asibitin Connaught, tsakanin karfe 9 na safe zuwa 5 na yammacin kowace rana domin dubawa.

Mr. Koroma ya alkawarta yiwa mamatan da ba a tantance su ba jana'izar karramawa, a garin Waterloo tsakanin ranekun 17 zuwa 18 na watan Agustar nan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China