in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uhuru Kenyatta ya sake zama shugaban kasar Kenya
2017-08-16 10:50:26 cri

A ranar 11 ga watan nan ne aka tabbatar da shugaban kasar Kenya mai ci Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da ya kammala a kwanakin baya. Akwai dai dalilai da ake ganin su ne suka sanya shugaba Kenyatta lashe wannan zabe, to amma dalili mafi muhimmanci shi ne, nasarorin da ya samu ta fuskar raya tattalin arziki a wa'adin aikinsa na farko a matsayin shugaban kasar. A shekaru 4 da suka wuce, matsakaicin karuwar tattalin arzikin Kenya ya kai kashi 5 cikin dari a kowace shekara, adadin da ya fi yawa daga matsakaicin matsayin wasu kasashen dake nahiyar Afirka.

A ranar 31 ga watan Mayu ne aka kaddamar da layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi a Kenya wato SGR a takaice, wanda wani kamfanin kasar Sin ya taimaka wajen shimfida shi. Wannan layin dogo ya zama na farko a tarihin Kenya cikin shekaru dari da suka wuce. A lokacin da ake shimfida shi, shugaba Kenyatta ya sha yin rangadin aiki, a wuraren aikin domin kara sanin yadda ake shimfida layin dogon.

Kenyatta yana sa muhimmanci wajen raya hulda a tsakanin kasarsa da Sin. Sakamakon taimakon da kasar Sin take bayarwa ya sa gwamnatin Kenyatta raya ababen more rayuwar jama'a sosai, an kyautata surar kasar ta Kenya. Alal misali, sabon zauren da matafiya ke yada zango a filin jiragen sama na Jomo Kenyatta ya fara aiki. An kuma kaddamar da hanyar mota mai saurin tafiya a tsakanin Thika da Mombasa. Mutane kimanin dubu 300 suna cin gajiyar aikin jigilar wutar lantarki a bakin tekun kasar ta Kenya. A watan Yulin bana, Kenya ta fara kafa yankin musamman na tattalin arziki mai suna Zhujiang, wanda ya zama irinsa na farko a kasar.

An haifi Uhuru Kenyatta a farkon shekaru 1960. Mahaifinsa shi ne Jomo Kenyatta, wanda shi ne shugaba na farko ga kasar ta Kenya. Mahaifinsa ya sanya masa suna "Uhuru", wato 'yancin kai a harshen Kiswahili. A wancan lokaci, Jomo Kenyatta ya jagoranci jama'ar Kenya wajen neman 'yancin kai a hannun 'yan mulkin mallaka na kasar Ingila. A shekarar 2002, a karon farko Uhuru Kenyatta ya shiga babban zabe, amma bai samu nasara ba.

A shekarar 2012, Kenyatta, wanda shi ne mataimakin firaministan kasar kuma ministan kudin kasar, ya tsara shirinsa na sake shiga babban zaben, amma kotun manyan laifuffuka ta duniya ta gabatar da kararsa, bisa zarginsa na aikata cin zarafin hakkin dan Adam.

Daga karshen shekarar 2007 zuwa farkon shekarar 2008, an samu tashe-tashen hankali a duk fadin Kenya, inda dubban mutane suka rasa rayukansu, yayin da wasu kimanin dubu 600 suka bar gidajensu. Mwai Kibaki, shugaban Kenya na wancan lokaci ya sanar da sake lashe zaben da aka kada, amma 'yan hamayyarsa sun zarge shi da yin magudi yayin kidayar kuri'un da aka kada, kuma suka ki amincewa da sakamakon zaben, a karshe dai, tashin hankali ya barke. Bangarorin 2 sun yi wa juna zargin yin kisan-kiyashi. A shekarar 2010, majalisar dokokin Kenya ta mika wannan batu ga kotun manyan laifuffuka ta duniya domin yin bincike.

A farkon shekarar 2012, kotun manyan laifuffuka ta duniya ta kai Kenyatta kara, bisa zargin aikata laifin yaki da cin zarafin dan Adam, tare da daukarsa a matsayin wanda ya kulla makarkashiyar barkewar tashin hankali, bayan babban zaben kasar na shekarar 2007. To sai dai shugaba Kenyatta ya yi watsi da wannan zargi

A wancan lokaci, Kenyatta ya jawo hankali sosai a cikin 'yan takarar babban zaben. Kasashen Amurka da Ingila ba su so ganin Kenyatta ya ci zaben, don haka suka yi ta barazana, ko da yake ba su cimma burin su ba. A shekarar 2013, Kenyatta ya lashe babban zaben, ya kuma zama shugaban Kenya mafi karancin shekaru a tarihi. Ana ganin cewa, sakamakon tsoma baki da kasashen yammacin duniya suka sha yi cikin harkokin cikin gida na Kenya, ya sa yawancin jama'ar Kenya zabar Kenyatta.

A karshen shekarar 2014, kotun manyan laifuffuka ta duniya ta soke shari'ar da ta fara kan shugaba Kenyatta.

Yanzu haka dai shugaba Uhuru Kenyatta, zai fara wa'adin aikinsa na biyu. Akwai kuma tarin kalubaloli dake gabansa, kamar tsadar kayayyakin masarufi dake addabar 'yan Kenya, da tarin matasan kasar dake neman ayyukan yi, don haka dai da sauran rina a kaba a yakin da ake yi da cin hanci da karbar rashawa, bai kuma dace a yi kasala wajen yaki da ta'addanci ba. Dukkan wadannan kalubalolin masu wuyar warware ne a gare shi.

A cikin alamar da ke shaida kasar ta Kenya, an rubuta kalmar Kiswahili ta "Harambee", wato hadin kai da harshen Hausa. Idan har a nan gaba Kenyatta na fatan kara sada jama'arsa da alherai, to ko shakka babu sai ya hada kan karin sassan jama'arsa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China