in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jajantawa babban birnin kasar Saliyo dake fama da bala'in zaftarewar laka da ambaliyar ruwa
2017-08-15 20:44:49 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, zaftarewar laka da ambaliyar ruwa da suka auku a yankin birnin Freetown na kasar Saliyo sun haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama, tare da hasarori da dama, kuma kasar Sin na jajantawa Saliyo da yankin da wannan annoba ta auku.

Bayan faruwar bala'in, wasu kamfanonin kasar Sin dake wurin sun halarci aikin bada ceto, da samar da wasu na'urori bisa bukatun gwamnatin kasar Saliyo, wannan ya shaida zumunta dake tsakanin jama'ar Sin da Saliyo. Kuma idan har kasar Saliyo ta bukata, Sin a shirye take ta kara goyo mata baya wajen samar da gudummawar da ta dace. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China