A wannan rana a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, a yayin yakin duniya na biyu, sojojin kasar Japan sun kai hari mai tsanani ga jama'ar kasar Sin. Akwai shaidu a tarihi, wadanda ba za a iya musanta su ba. Kuma Sin tana fatan kasar Japan za ta duba hakikanin tarihi game da harin ta kan kasar Sin, ta girmama jama'ar kasashen Asiya ciki har da kasar Sin, wadanda suka sha fama sakamakon hare haren mayakan kasar ta Japan. (Zainab)