in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tayi Allah wadai da tashin hankali a Charlottesville kana ta aike da sakon ta'aziyya
2017-08-15 11:26:38 cri
Mai Magana da yawun sakatare janar na MDD Farhan Haq, ya bayyana cewa babban magatakardan MDD Antonio Guterres, yayi Allah wadai da hatsaniyar data barke da kuma fadan nuna wariyar launin fata a Charlottesville, na jahar Virginia na kasar Amurka, kana ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalai da masoyan wadanda tashin hankalin ya rutsa dasu.

Farhan Haq yace, suna nuna adawa da duk wani batu da ya shafi nuna wariya ko banbancin launin fata, yace sun yi amanna babu wata mafaka a cikin dukkan al'umma da za'a saurarawa masu halayyar tada rikici don nuna wariyar launin fata, ko nuna banbancin kabila, ko nuna kyama ko kuma cin zarafin bil adama irin wanda aka gani a Charlottesville, na jahar Virginia a 'yan kwanakin nan.

Wata mata 'yar shekaru 32, mai suna Heather Heyer, 'yar yankin Charlottesville, an hallaka ta bayan ta samu munanan raunuka a ranar Asabar, a sakamkaon wata mota da ake zargin wani farar fata ya haura ta kan wasu gungun jama'a, inda suke yin zanga-zangar nuna adawa da zanga-zangar da 'yan neo-Nazis da white-supremacists suka yi a baya ta nuna rashin amincewa da tunbuke tsohon kwamandan rundunar juyin juya hali a lokacin yakin basasa na Amurka janar Robert E. Lee, yanzu dai an danganta lamarin da nuna wariyar launin fata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China