170815_kafofi-sin-afirka-bilkisu.m4a
|
Cikin jawabin da ya gabatar wajen taron, mista Guo Weimin ya ce,
"Akwai karancin fahimtar juna tsakanin bangarorin Sin da Afirka, idan aka kwatanta da ci gaban da aka samu a fanin hadin gwiwar bangarorin 2. Saboda haka ya ba da shawarar kara yin hadin kai, tsakanin kafofin watsa labaru na bangarorin 2, domin tabbatar da samar da murya mai adalci da sanin ya kamata. "
Dangane da yadda za a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kafofin yada labaru na Sin da Afirka, mista Guo Weimin ya ce,
"Ya kamata a karfafa fahimtar juna tsakanin kafofin watsa labarai na kasar Sin da na kasashen Afirka, tare da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin daukaka mu'amalar bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi. Sannan kuma, bangarorin biyu su bayyana ra'ayoyinsu yadda ya kamata a duniya bisa hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakaninsu."
A nasa bangare Timothy Olariwaju, babban editan jaridar' the Sun' ta kasar Najeriya, cewa ya yi
"har yanzu a Najeriya, mutane da yawa suna sauraron labarai ta hanyar rediyo. Kuma bisa kafa sashen Hausa da gidan rediyon kasar Sin ya yi, ya sa 'yan Najeriya jin dadin sauraron bayanan da ake watsa wa ta harshen Hausa, wadanda suka shafi al'adun kasar Sin, da ayyukan gini da Sinawa suke yi a Najeriya. kokarin da CRI ke yi wajen watsa labarai ga kasashen Afirka yana tare da nasarori, ya kuma yi fatan ganin gidan rediyon ya fara watsa labarai ga karin kasashen dake nahiyar Afirka."