Rahotanni sun bayyana cewa, Dalai Lama ya soke tafiyar da ya shirya zuwa Botswana ne a tsakiyar watan nan na Agusta, bisa dalilai na rashin lafiya.
Da take tsokaci game da hakan, Hua Chunying ta ce Sin na daukar alakar kawancen ta da Botswana da matukar muhimmanci, tana kuma fatan hakan zai dore, ya kuma kai ga haifar da ci gaba mai dorewa tsakanin sassan biyu. (Saminu Alhassan)