Yau Litinin, mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda ke cigaba da ziyarar aiki a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda ya yi tattaki zuwa wasu kamfanoni guda biyu, wato kamfanin saka tufafi na Shangtex, da kamfanin mulmula karafa na Baowu. Mai martaba sarkin ya bayyana aniyarsa ta karfafa hadin-gwiwa da yin mu'amala tare da kamfanonin kasar Sin, musamman a fannonin masana'antu, cinikayya, kiwon lafiya, al'adu, ilimi da sauransu.