Mai martaba sarkin Kano ya gana da mataimakiyar shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta birnin Shanghai
Yau Litinin da safe, mai martaba sarkin Kano wanda a yanzu haka yake ziyara birnin Shanghai na kasar Sin, Muhammadu Sanusi II, ya gana da mataimakiyar shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta birnin Shanghai, madam Zhao Wen, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayi kan karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin Kano da Shanghai, musamman a fannonin zuba jari, masana'antu, cinikayya, kiwon lafiya, ilimi, al'adu da sauransu.