Yau Lahadi, mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ke ci gaba da ziyarar aiki a kasar Sin, inda ya bar birnin Shenzhen ya iso birnin Shanghai, cibiyar tattalin arzikin kasar Sin. Mai martaba sarki ya ziyarci babban dakin nune-nunen tsarin birnin Shanghai, inda ya nuna yabo ga babban ci gaban da Shanghai ta samu. Wannan shi ne karo na farko da mai martaba sarkin ya kai ziyara a birnin na Shanghai.(Murtala)