in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na Sin da Najeriya na fatan karfafa mu'amala tsakaninsu
2017-08-11 13:36:16 cri

A jiya Alhamis 10 ga watan nan ne aka gudanar da taron kara wa juna sani, tsakanin kafofin yada labaru na kasashen Sin da Najeriya a Abuja, fadar mulkin kasar Najeriya. Mataimakin direktan ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin Mr. Guo Weimin, da shugaban jaridar Leadership ta Najeriya Sam Nda Isaiah, da uwar gida Olufunke Adenike Egbemode, shugabar kungiyar editocin Najeriya, da sauran shugabanni da editoci da 'yan jaridu kimanin dari 1, daga kafofin yada labaru na Najeriya ne suka halarci taron.

A yayin taron, Mr. Guo Weimin ya ce, makasudin ziyarar su a Najeriya a wannan karo shi ne, kara fadada mu'amala a tsakaninsu da sassan gwamnati, da masu aikin jarida, da fararen hula na Najeriya, kan batutuwa daban daban, a wani mataki na cimma matsaya daya, wajen aiwatar da muhimmin ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma kan bunkasa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, tsakanin kasashen Sin da Najeriya, da kuma sakamakon da aka samu a yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu, ta yadda za a iya ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba, da kuma kai hadin gwiwa da mu'amala da ake yi tsakanin kasashen biyu a fannonin aikin jarida, da abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum zuwa wani sabon matsayi." Sannan bisa sabon halin da ake ciki yanzu, kan yadda kafofin yada labaru na kasashen Sin da Afirka za su iya habaka huldar abokantaka, da karfafa hadin gwiwa da mu'amala tsakaninsu domin neman ci gaba tare a nan gaba, Mr. Guo Weimin ya gabatar da shawarwari uku, wato, daga farko dai, ya ce ya kamata a yada labarun dake shafar bunkasa huldar abokantaka tsakanin Sin da Najeriya, domin fararen hula na kasashen biyu su iya fahimtar juna. Sannan, ya kamata a kirkiro sabbin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labaru na kasashen biyu, domin su ci gaba tare. Daga karshe ya ce, ya kamata a kara yin hada kai tsakanin sassan, domin inganta ikon ba da ra'ayoyin kasashe masu tasowa a dukkanin fadin duniya.

A nata bangaren, madam Olufunke ta ce, a da ba ta da masaniya sosai game da kasar Sin. Amma tsakanin renakun 23 zuwa 28 ga watan Yulin bana, ita da sauran mambobin kungiyarta guda 4, sun ziyarci sassan kasar. Kuma isarta birnin Beijing, ya ba ta damar fahimtar kasar Sin yadda ya kamata. Ta ce ci gaban da kasar Sin ta samu ya wuce abin da take tunani a zuciya. Ta ce da ba dan ta gani da idonta ba, lalle, ba za ta amince da ci gaban da kasar Sin ta samu cikin sauri fiye da kima ba.

Uwar gida Olufunke ta ce ta yi mamakin matuka musamman ganin yadda kafofin yada labaru na kasar Sin suke samun ci gaba. Lokacin da take nan Beijing, ta ziyarci gidan rediyon kasar Sin CRI, da gidan jaridar People's Daily. Ta ce sashen Hausa na CRI ya burge ta sosai. A ganinta, aikin watsa labaru da harsunan waje yana da muhimmanci matuka. Ta kuma yi fatan kasarta za ta iya yin hadin gwiwa da kafofin yada labaru na kasar Sin, musamman a fannin koyar da harshen Sinanci a Najeriya.

Bugu da kari, masu aikin jarida na kasar Najeriya wadanda suka halarci taron sun ba da ra'ayoyinsu da shawarwarinsu. Mr. Sam Nda Isaiah, shugaban jaridar Leadership ya ce, masu aikin jarida na Najeriya suna fatan kara yin hadin gwiwa da takwarorinsu na Sin. Yana fatan za a iya samun wasu sabbin hanyoyin hadin gwiwar kafofin watsa labaru na Sin da Najeriya, ta yadda kasar Sin za ta iya samun sahihan batutuwa na Najeriya, kana Najeriya ma za ta iya kara fahimta yadda kasar Sin take samun ci gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China