in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya damu game da mutuwar 'yan cin rani masu yawa a Afrika
2017-08-11 10:33:37 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya nuna matukar damuwa game da wani rahoto da ya samu cewa, masu safarar bil Adama da suka kwaso bakin haure daga yankin Horn of Afirka zuwa kasar Yemen, inda suka tilasta su tsallake cikin teku, lamarin da ya yi sanadiyyar bacewar mutanen sama da 50.

Hukumar kula da makaurata ta kasa da kasa IOM, wacce ke karkashin kulawar MDD, ta sanar da cewa baya ga hasarar rayuka da aka samu a kasashen Habasha da Somaliya a a ranar Laraba, an tilastawa wasu bakin haure su 180 ratsawa ta tekun Yemen, kasar dake fama da tashin hankali. An tsinci gawarwakin mutane 5, kana wasu 50 kuma sun bace bat.

Stephane Dujarric, mai Magana da yawun mista Guterres, ya shedawa 'yan jaridu a hedkwatar MDDr cewa, hukumar ta nuna damu game da yawaitar mutuwar bakin hauren a tekun Yemen cikin kwanaki biyun da suka wuce, inda masu safarar mutanen ke yin jigilarsu ta kananan jiragen ruwa inda suke ratsawa ta tekun.

Dujarric ya ce, sakatare janar na MDDr ya damu matuka game da aukuwar lamarin. Don haka ya bukaci kasashen duniya da su ci gaba da daukar matakai na hana barkewar tashin hankali, wanda shi ne ke tilasta mutane barin garuruwansu na asali inda suke jefa rayuwarsu cikin garari.

Mista Dujarric ya kara da cewa, ya zama tilas a dauki matakai na yin amfani da dokoki da bin hanyoyin da suka dace don hana mutanen dake jefa rayuwarsu cikin musifa, wadanda suke bukatar samun kariya ta kasa da kasa.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China