Rahoton kungiyar likitocin na gari na kowa MSF da ya bayyana adadin a jiya, ya ce bangarori na ci gaba da nuna adawa da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai.
Tun bayan hambarar da Francois Bozize a watan Maris din 2013 da kawancen kungiyar 'yan tawaye ta Seleka ta yi, da kuma matsin lamba daga kasashen ketare, kasa da shekara guda bayan nan, kasar Afrika ta Tsakiya ta tsunduma cikin rikici, duk da kafa sabbin tsare-tsaren demokradiyya da aka yi, ciki har da lashe zaben shugaban kasa da Faustin-Archange Touadera ya yi cikin watan Fabrerun bara a Bangui. (Fa'iza Mustapha)