in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin inshora na Huatai ya kulla kasuwanci da kamfanin kirar jiragen sama na COMAC
2017-08-10 10:06:11 cri

Kamfanin inshora na Huatai dake kasar Sin, ya sanya hannu kan wani tsarin kasuwanci na zuba jari ga kamfanin kirar jiragen sama na COMAC.

Bisa tsarin kasuwancin da sassan biyu suka sanyawa hannu, Huatai zai zuba jari ga COMAC wanda yawansa ya kai Yuan biliyan 15, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.25.

Karkashin yarjejeniyar kamfanin COMAC wanda shi ne irinsa na farko a kasar Sin dake kera jiragen dakon fasinjoji da ke da hedkwata a Shanghai, zai amfana da jarin cikin wa'adin shekaru 10, tare da damar sake sabunta kwangilar bayan cikar wa'adinta.

Wannan ne dai karon farko da COMAC ya kulla irin wannan kwangila da wani kamfani na daban.

Wasu alkaluma na hukumar gudanarwar kamfanonin inshora sun tabbatar da cewa, ya zuwa karshen watan Yunin da ya gabata, kamfanonin inshora na da jarin da yawansa ya kai Yuan trilian 16.4.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China