Bisa gayyatar da Kungiyar sada zumunta tsakanin al'ummar kasar Sin da sauran kasashen duniya wato CPAFFC ta yi masa, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, zai kawo ziyara kasar Sin daga yau 10 ga wata, zuwa ranar 17 ga watan nan da muke ciki, inda zai ziyarci biranen da su ka hada da Guangzhou da Shenzhen da Shanghai da kuma Beijing.
Mahaifin Muhammadu Sanusi na biyu, shi ne jakadan Nijeriya na farko a kasar Sin, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Nijeriya a shekarar 1971. (Maryam)