in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar CPPCC ya yaba da nasarorin da yankin Mongolia ta gida ya samu cikin shekaru 70 da suka gabata
2017-08-08 20:29:36 cri
Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng ya yaba da tarin nasarorin da yankin Mongolia ta gida ya samu cikin shekaru 70 da suka gabata, yana mai fatan cewa,yankin mai cin gashin kansa zai kara samar da rayuwa mai inganci ga jama'arsa.

Mr. Yu ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin da ya jagoranci wata tawaga mai mutane 63 don bikin murnar cika shekaru 70 da kafa yankin. Ya kuma nanata muhimmancin da aka dora a kan jagorancin JKS, wanda ya ce ita ce ginshikin hada kai da jagorancin dukkan kabilun kasar, da bin tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin.

A ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1947 ne, an kafa yankin Mongolia ta gida mai cin gashin kansa karkashin jagorancin JKS. Yankin mai fadin murabba'in kilomita miliyan 1.18, ya kai kashi 12 cikin 100 na fadin kasar Sin. Kana yawan 'yan kabilar Mongoliya a yankin ya kai miliyan 4.6, kimanin kashi 1 bisa biyar da yawan al'ummar shiyyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China