in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya shugaban Rwanda murnar sake lashe zabe
2017-08-08 19:58:45 cri
A yau Talata ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aikawa takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame sakon taya murna, dangane da sake zabarsa da aka yi a matsayin shugaban kasar.

A cikin sakon, shugaba Xi ya ce, yana dora muhimmanci a kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana zai kara kokari don ganin ya karfafa dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da kasar Rwanda, ta yadda za su kara cimma nasarori wadanda za su dace da muradun kasashe da ma al'ummominsu,da kuma daga matsayin hadin gwiwar kasashen biyu.

A ranar Asabar din da ta gabata ce aka sake zabar Kagame da babban rinjaye a zaben shugaban kasar da aka yi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China