in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarin wasu mutanen da suka yi kokarin gina filin dashe na itatuwa a kasar Sin
2017-08-08 12:35:55 cri

wani wurin dake da tazarar kilomita kimanin 200 zuwa arewacin birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, akwai wani filin dashe na itatuwa da ake kiransa "Sai-Han-Ba". Sai dai idan ka tafi wurin wasu shekaru 55 da suka wuce, za ka ga tamkar hamada ce, abin da za a iya gani rairayi ne kawai. Amma wadanne mutane ne suka taimaka wajen gyara muhallin wurin?

Yu Shitao da matarsa Fu Lihua dukkansu suna aiki a filin dashe na itatuwa na Sai-Han-Ba. Yu, shugaba ne ga wata ma'aikatar sarrafa itatuwa, yayin da matarsa Malama Fu tana aiki wajen wata cibiyar nazarin fasahar dasa itatuwa. Bayan da Madam Fu ta yi karatu har ma ta samu digiri na biyu, ta yi wasu shekaru 3 tana aiki a cikin wani kamfnin dake Beijing. Amma a karshe ta yi murabus domin koma wurin da mijinta yake aiki. Har zuwa yanzu, a cewar Madam Fu, ba ta ji dadin zama a gandun dashe na itatuwa sosai ba.(1)

"Akwai abubuwan da ba a iya sabawa da su. Misali, a cikin gari muna da wuraren nishadi da za a iya zuwa har ma da dare, ban taba barci kafin karfe 11 ba. Amma a nan, bayan kammala aiki, ina huta a gida ne kawai. Zaman rayuwa ya gundure ni."

Kamar Madam Fu, ma'aikatan filin dashe na itatuwa na Sai-Han-Ba suna fuskantar zaman rayuwa mai cin rai, amma magabantansu sun fi shan wahalhalu, ganin yadda a lokacin ba a samu kayayyakin more rayuwa masu inganci ba tukuna. Guo Zhifeng, shugaban wata tashar kare itatuwa ne, ya kuma gaya ma wakilinmu cewa,"A lokacin, idan an yi ruwa, motar mu ba ta iya shiga ciki, don haka ba a samun abincin da ake bukata. Wani lokaci ma a kan yi kwanaki 6 zuwa 7 ana ruwa, babu nama da kayan lambu, sai dai mu ci shinkafa kawai. Sa'an nan akwai matsalar rashin wutar lantarki, da kadaici."

Wahalhalun da ake fuskanta a wurin sun sa wasu mutane sun gudu, amma sauran ma'aikata su zabi ci gaba da aiki a can. Mista Cheng Shun, shugaban cibiyar nazarin fasahar dasa itatuwa, shi ma ya zabi tsayawa."Da ma na ayyana cewa idan na kasa jurewa wahalar, zan bar wurin. Amma a karshe na fara kaunar sana'ar dasa itatuwa, kuma na lura bisa ilimin da na samu ina iya samar da gudunmowa. Don haka na tsaya. Yanzu a gani na zabin da na yi daidai ne, domin na taimaka wajen gyara muhallin wurin."

A nashi bangare, Guo Zhifeng, shi ma ya tsaya a wurin, kuma ya shiga aikin kau da kwarin da su kan lalata itatuwa. Shi da abokan aikinsa sun tsara wata sabuwar hanyar kandagarkin bullowar kwari, kuma sun dogaro kan matakan da ba za su lalata muhalli ba, maimakon yawan amfani da maganin kashe kwari. Ta wannan hanya, sannu a hankali, an samu damar shawo kan matsalar kwari a filin dashe na itatuwa na Sai-Han-Ba, gami da kyautata muhallin wurin. A cewar Guo Zhifeng,"Tsakanin shekarar 2014 da ta 2016, mun yi nazari kan halittu iri-iri da ake samu a gandun dashen itatuwan nan namu, inda muka gano wani kwaro na musamman, wanda ba ya iya rayuwa a wuri mai gurbataccen muhalli, sai a wuri mai tsabta sosai yake rayuwa. Wannan alama ce da ta nuna cewa muhallin wurin na da kyau. Muna farin ciki kwarai."

Bisa gudanar da ayyuka na yau da kullum, ma'aikatan filin dashe na itatuwa na Sai-Han-Ba su ma sun samu damar cimma burinsu. A cewar Mista Cheng Shun,"Ya kamata a yi kokarin nuna wata daraja ta musamma, wadda ta sha bamban da ta sauran mutane. Ga misali, kowa na iya kidaya. Amma idan ka iya daidaita wasu matsaloli bisa hazakarka a fannin kidaya, to, hakan zai samar da daraja."

Yu Shitao ya fara aiki a gandun itatuwa na Sai-Han-Ba a shekarar 2005. Bisa fasahohin da ya koya a cikin jami'a, da karin kwarewar da ya samu a wurin aiki, Yu ya taimakawa inganta fasahohin dasa itatuwa. Yanzu cikin itatuwan da aka dasa, fiye da kashi 95% ne za su iya girma. Irin kaunar da Yu ya nuna wa filin itatuwan ta burge matarsa Fu Lihua. Har ma ta ce ba ta taba nadamar zuwa zama a gandun itatuwan ba.

Yanzu Fu ta yi shekaru 6 tana aiki a filin itatuwa na Sai-Han-Ba, yayin da mijinta ya yi shekaru 12 yana can. Wannan wuri ya riga ya zama gidansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China