Sai dai ya ce ba zai yiwu a rufe nan take ba, domin dole sai an dauki wasu matakan doka kafin aiwatar da shirin.
Ayoub Kara ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, yana da niyyar ya bukaci ofishin watsa labarai na gwamnati, wato ofishin dake da alhakin bada katin izinin watsa labarai, ya kwace lasisin wakilan Al-Jazeera dake Isra'ila.
Ministan ya ce ya tuntubi kamfanonin dake nuna tashoshin talabijin na tauroron dan Adam, kuma ya bukaci su cire Al-jazeera daga cikin jerin tashoshinsu.
Ayoub Kara ya ce ya yanke shawarar daukar mataki a kan Al-Jazeera ne, saboda goyon bayan ta'addanci da take yi.
Ya kuma zargi Al-Jazeerar da rura wutar rikici da ya kai ga asarar rayukan 'yan kasar, yana mai bada misali da harin da aka kai ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata a wajen harabar masallacin Al-Aqsa dake gabashin birnin Jerusalam, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda biyu. (Fa'iza Mustapha)