in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar dakarun Sin a gasar sarrafa tankokin yaki ta kai matsayin kusa da na karshe
2017-08-07 09:55:39 cri
Rahotanni daga kasar Rasha na cewa, tawagogin dakarun kasar Sin guda uku dake halartar gasar sarrafa tankokin yakin soji ta kasa da kasa ta bana, sun kai ga matsayin kusa da na karshe.

A bana gasar dake gudana a Rasha ta samu halartar tawagogin dakaru 76 daga kasashe 19, wadanda suka fafata a zagayen farko tsakanin ranekun 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta, tuni kuma tawagogi 12 suka kai ga zagayen kusa da na karshe na wannan gasa.

Ana sa ran gudanar da matakin kusa da na karshe na gasar ne cikin kwanaki uku tun daga gobe Talata. Dakarun dake fafatawa domin lashe gasar na nuna kwarewarsu ne a fannin sarrafa tankokin yaki, tare da harbin wasu abubuwa da aka sanya bisa nuna kwarewa a yanayi mai sarkakiya.

Da yake tabbatar da shirinsu na lashe gasar, daya daga cikin sojojin kasar Sin Guo Shengdong, ya ce sun kimtsawa gasar yadda ya kamata, kuma ba abun da suke jira illa shiga zagayen karshe.

A nasa bangare daya daga masu alkalancin gasar Roman Binyukov, cewa ya yi sojojin kasar Sin sun samu cikakken horo, kuma sun kara samun maki a bana. Kuma alamu na nuna cewa za su cimma babbar nasara a karshen gasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China