in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IFAD ya bayyana shirin kasar Sin na yaki da talauci da cewa abin koyi ne ga sauran kasashe
2017-08-04 11:17:49 cri
Sabon shugaban asusun raya ci gaban ayyukan gona na kasa da kasa (IFAD) Gilbert Houngbo, ya bayyana a cikin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, nasarar da kasar Sin ta samu na tsame miliyoyin 'yan kasar daga cikin kangin talauci cikin shekaru ashirin ya zama abin koyi ga sauran kasashen duniya wajen sauya fasalin tattalin arzikinsu.

Shugaban na IFAD ya bayyana cewa, ya kasance tamkar wata alama ce a fili, tsarin fasalin tattalin arzikin kasar Sin zai iya zama wata dama ce da kasashe masu tasowa da za su iya yin koyi don cimma nasarori masu yawa.

Houngbo, wanda tsohon firaiminista ne na kasar Togo ya bayyana cewa, hakika, akwai abubuwan koyi masu yawa da za'a koya daga irin ci gaban kimiyya da kasar Sin ta samu, alal misali, yadda kasar ke amfani da hanyoyin yaki da matsalar ambaliyar ruwa ko kuma matsalar fari, wanda hakan za'a iya yin amfani a wadannan dabaru a wasu wuraren na daban.

Sannan ya buga misali da yadda kasar Sin ke raya birane, da saurin bunkasuwar tattalin arziki da kasar Sin ta samu a 'yan shekarun nan, inda kasar ta shawo kan matsalar kwararar mutane zuwa birane ta hanyar bunkasa ayyukan noma a yankunan karkara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China