Kakakin Palasdinawan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, don mayar da martini ga kalaman da aka ruwaito Netanyahu na cewa, wai yammacin kogin Jordan da gabashin birnin Kudus bangaren Isra'ila ne, yana mai cewa, matsugunan Yahudawa da Isra'ila take ginawa a yammacin birnin Kudus sun sabawa doka, kana yammacin kogin Jordan da zirin Gaza, dukkansu yankunan Palasdinawa ne.
A don haka, kakakin hukumar Palasdinawan ya yi kira ga mahukuntan Isra'ila da su hanzarta dakatar da gine-ginen, wadanda ya ce suna iya wargaga kokarin da ake yi na warware wannan matsala ta hanyar kafa kasashe biyu. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya, musamman Amurka da ta sanya baki, kana ta dakatar da matakin Isra'ila na gina matsugunnan Yahudawa, yana mai gargadin cewa, matakin Isra'ilan na iya haifar da mummunan sakamako. (Ibrahim Yaya)