A yayin ganawar, Yang Jiechi ya bayyana cewa, bayan da kasashen Sin da Gambia suka sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu a watan Maris na shekarar 2016, sun kuma maido da hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. Kasar Sin tana fata hada kai da kasar Gambia wajen kara yin imani da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwarsu, da kara yin mu'amalar al'adu don inganta dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Gambia Mr. Darboe ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar kawa ce dake nuna goyon baya da samar da gudummawa ga nahiyar Afirka, kana aminiyar kasar Gambia ce, kasar Gambia tana nuna godiya ga kasar Sin bisa ga gudummawar da ta dade tana samar mata a a fannoni daban daban. Sabuwar gwamnatin kasar Gambia tana martaba manufar Sin daya tak a duniya. (Zainab)