in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: ya kamata a kara inganta karfin sojoji ta yada zai dace da yanayin kasar Sin
2017-08-01 12:51:09 cri

A yau 1 ga watan Agusta a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, aka gudanar da taron murnar cika shekaru 90 da kafuwar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin PLA, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar, Xi Jinping ya halarci taron tare da yin wani muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya jaddada cewa, muddin ana bukatar samarwa al'ummar Sinawa ci gaba gami da rayuwa mai inganci, tilas ne a raya sojojin jama'ar kasar a matsayin sojoji da suka fi karfi a duniya, ya kamata a ci gaba da martaba manufofi da aka tsara tun farko da samun bunkasuwa, da daukar matakan inganta karfin sojoji da yadda zai dace da yanayin kasar Sin, da kuma sa kaimi ga inganta karfin sojojin kasar yadda ya kamata.

"A yau ne aka bude taron murnar cika shekaru 90 da kafuwar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin PLA."

Taron ya kuma samu halartar dukkan zaunannun membobi 7 na hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin, da shugabannin kasa da na jam'iyyar kwaminis ta Sin wadanda suke nan birnin Beijing, da kuma wakilai daga bangarori daban daban kimanin 3000. Da karfe 10 na safiyar wannan rana ce, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya sanar da bude taron. Dukkan mahalarta taron sun mike tsaye inda suka rera taken kasar Sin. A muhimmin jawabin da ya gabatar shugaba Xi Jinping ya waiwayi tarihin sojojin jama'ar kasar Sin dake karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da hangen nesa ga bunkasuwar aikin tsaron kasar da karfin sojojin kasar. Xi ya bayyana cewa,

"A cikin shekaru 90 da suka wuce, rundunar sojan kasar Sin ta samu ci gaba karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar, kuma an kafa jerin ka'idoji na kula da rundunar tare da bunkasa dabaru na kare lafiya da dukiyoyin al'umma, kuma wannan shi ne manufar da rundunar ke bi wajen samun nasara da kuma alkiblar da rundunar za ta bi har abada."

Mr. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar shi zai tabbatar da manufar rundunar sojan kasar, an kuma yi imanin cewa, shi ne abin da zai taimaka ga ci gaban rundunar. Ya zama dole rundunar sojan kasar ta dukufa wajen yin gyare-gyare ba tare da kasala ba, kuma ta nuna bajinta wajen samun nasarar yaki. Haka kuma ya zama dole rundunar ta martaba manufar bautawa al'ummar kasar a ko da yaushe.

Xi Jinping ya ce, bayan babban taro karo na 18 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, rundunar sojin jama'a wato PLA ta kirkiro sabbin ka'idojin ba da jagoranci ga aikin soja, ta kuma tsara sabbin manufofin aikin soja bisa la'akari da yanayin da ake ciki. Sannan an kara mai da hankali wajen bunkasa rundunar soja bisa ka'idojin siyasa, ta yadda za a zurfafa gyaran fuskoki a harkokin tsaron kasa da na rundunar soja. Sakamakon haka, an samu ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi wajen gina tsarin soja bisa halin da kasar Sin ke ciki. A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na fuskantar damar da watakila ba za a iya samu a kullum ba, a yayin da take fuskantar kalubaloli iri iri. Amma yaya za a ci gaba da gina rundunar soja mai karfi a nan gaba? Mr. Xi Jinping ya nuna cewa,

"Idan ana son kara gina rundunar soja mai karfi, dole ne a tsaya tsayin daka kan matsayin kasancewar rundunar soja ta PLA a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, da tabbatar da cewa rundunar PLA ta bin umurnin jam'iyyar. Sannan dole ne jam'iyyar CPC ta tsaya ta kuma fito da sabon tunanin bunkasa aikin soja. Bugu da kari, dole ne a kara mai da hankali kan yadda za a gina rundunar soja mai karfi sosai wadda take bin umurnin jam'iyya, domin tabbatar da samun nasara a duk wani yaki da ka iya tasowa a nan gaba. Haka kuma, dole ne a tsaya kan matsayin bunkasa rundunar soja bisa tunanin siyasa da kuma doka domin kara karfin soja ta hanyoyin yin gyare-gyare da kuma fasahohin zamani, ta yadda za a iya zamanintar da harkokin tsaron kasa da na rundunar sojan PLA. Bugu da kari, dole ne a kara yin kokarin neman ci gaban harkokin soja da na farar hula tare, domin gina wani tsari mai karfi game da harkokin tsaron kasar inda rundunar soja da al'ummar kasar za su iya taka rawa cikin hadin gwiwa. Daga karshe, dole ne rundunar soja ta PLA ta martaba ka'idojin da aka gindaya mata na bauta wa al'ummar kasar domin ta samu amincewa da goyon baya da kuma kauna daga jama'a a kullum."

Shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen wanzar da zaman lafiya da bada taimako ga raya harkokin da suka shafi duniya baki daya, tare kuma da kiyaye doka da oda. Haka kuma, sojojin kasar Sin na bayar da babbar gudummawa ta fuskar aikin shimfida zaman lafiya a duniya. Xi ya jaddada cewa:

"Sinawa mutane ne masu kaunar zaman lafiya, kana kasar Sin ba za ta kai hari kan yankunan wasu kasashe duniya ba, amma duk da haka, muna da imanin samun galaba kan duk wani yunkuri na kawowa kasar Sin hari. Ko da yaushe, kuma a kowane hali, kasar Sin ba za ta yarda da duk wani yunkuri da wani mutum ko wata kungiya ko jam'iyya za su yi, na kawowa Sin baraka ba. Kana, kasar Sin ba za ta amince da duk wata barazana da za'a mata game da 'yancinta na mallakar yankuna da tsaro gami da ci gabanta ba. Ya kamata rundunar sojan kasar Sin ta tsaya kan rungumar shugabancin jam'iyyar kwaminis gami da tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin, da kuma nacewa ga kiyaye 'yancin mallakar yankunanta da tsaron kasa gami da ci gabanta. Har wa yau, ya kamata sojojin kasar Sin su yi kokarin kiyaye zaman lafiya a yankuna gami da fadin duniya baki daya."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China