in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin faretin murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA
2017-07-31 14:57:27 cri

A jiya Lahadi 30 ga wata ne, aka yi bikin faretin murnar cika shekaru 90 da kafa rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ta PLA a sansanin horas da soja dake garin Zhurihe na jihar Mongoliya ta gida a nan kasar Sin. Bambancin da ke tsakanin bikin fareti na wannan karo da na baya shi ne, sojojin da suka halarci bikin faretin wannan karo, sojoji ne da ke samun horon aikin soja, don haka bikin ya yi kama da fagen daga.

A sararin sama na sansanin horar da soja na garin Zhurihe, ana iya jin babban amo, jiragen sama masu saukar ungulu 40 suna shawagi a filin bikin faretin. Gaba daya akwai rundunoni 45, rukunonin tinkarar abokan gaba 9 baya ga sojoji dubu 12 da suka shiga bikin.

Wannan shi ne karo na farko da rundunar sojojin kasar Sin ta yi faretin soja a sansanin soja, ba kamar yadda a kan yi bikin a baya a bainar jama'a ba, kana a wannan karo babu rukunin soja da fareti ko maci, babu kungiyar 'yan badujala, kuma babu masu wake-wake. Ko a fannin nuna sojoji, ko a fannin nuna kayayyakin soja, bikin faretin dai ya nuna karfin sojan kasar Sin ne kawai.

A cikin rukunin tinkarar abokan gaba a kasa, Ding Hui wanda ya shiga bikin fareti har sau uku ya tuka tankar yaki kirar 99A da ke kan gaba a kasar Sin zuwa filin faretin. Ding Hui yana ganin cewa, bikin faretin na wannan karo ya sha bamban da na baya. Ya kara da cewa,

"Wannan shi ne karo na farko da na halarci bikin fareti a sarari. A bikin fareti na baya, inda mu kan yi tafiyar kilomita goma a ko wace sa'a a kan titin Chang'an, amma a bana saurinmu ya karu zuwa kilomita 15 a ko wace sa'a. Ban da wannan kuma, mun ajiye dukkan kayayyakin da mu kan yi amfani da su a lokacin samun horo a kan motocin yakinmu, kuma mun bude na'urar kallon waje da ta sansano haske. Bugu da kari, an bukace mu rataya bindiga, mu saka takalman yaki. Abin da ya sa muka ji kamar muna fagen yaki ne."

A sararin sama, wani rukunin jirgin saman yaki da takwaransa na abokan gaba da ya kunshi jiragen sama 15 na wucewa ta filin bikin faretin. A ciki, jiragen saman yaki da takwaransa na abokan gaba guda 7 kirar 11B sun harbo harsashin yaudarar makamai masu linzami na abokan gaba domin su bar hanyarsu, wanda ya jawo hankalin mutane sosai. Game da wannan, manazarci a sashen kula da kai hari ta sama na yankin yaki na tsakiyar kasar Sin Fan Huiyu ya bayyana cewa, an yi hakan ne domin nuna karfin sojan kasar Sin a fagen daga. Yana mai cewa,

"yayin da rukunin jirgin saman yaki da takwaransa na abokan gaba ya wuce filin faretin, jiragen saman yaki da takwaransa na abokan gaba kirar 11B sun harbo harsashin yaudarar makaman masu linzami na abokan gaba domin su bar hanyarsu, wannan ba wani abu ba ne. A yaki, harba irin wannan harsashin wata hanya ce mai matukar muhimmanci wajen sanya makamai masu linzami na abokan gaba su bata daga hanya."

Ban da wannan kuma, yadda aka tsara rukunonin tinkarar abokan gaba a faretin ya nuna dabaru da ake amfani da su don samun galaba a lokacin yaki. Wato a baya, a kan yin maci bisa nau'o'in rukunin soja, amma a wannan karo, an hada su tare, kuma an nuna rukunonin kamar yadda a kan yi a lokacin yaki. Game da wannan, Tang Ning, mataimakin hafsan hafsoshi na sojojin kasan yaki na tsakiyar kasar Sin ya bayyana cewa, wannan ya nuna yadda sojojin kasar Sin za su kasance a lokacin yaki a zamanin yau. Ya kara da cewa,

"A yayin bikin faretin, hadaddiyar rudunar sojan kasa ta hada da sojojin kai farmaki daga sama, sojojin laima, sojan rundunar jiragen ruwa da ke gudanar da yaki a kasa da dai sauransu, a maimakon rundunar sojan kasa kawai. Haka kuma hadadiyyar rundunar sojan sama ta hada da sojojin sama, sojan rundunar jiragen ruwa da ke gudanar da yaki ta sama, a maimakon sojan sama kawai."

Bikin fareti na wannan karo, shi ne na farko da sojojin kasar Sin suka yi don murnar ranar kafuwar PLA, wanda ya nuna wa duniya karfin sojan kasar Sin sosai. Han Weiguo, babban mai ba da umurni na bikin kuma babban kwamandan kula da harkokin yaki na kasar Sin ya bayyana cewa, sojojin kasar Sin za su bi umurnin Shugaba Xi Jinping, za su mai da hankali kan horo ko da yaki ka iya barkewa. Idan har bukatar hakan ta taso, za su shiga yaki ba tare da bata lokaci ba, kuma za su yi kokari don samun nasarar yaki.(Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China