Maniyyatan kasar Sin sama da dubu 12 ne za su gudanar da aikin hajjin bana a kasa mai tsarki wato Makka, wadanda za su tashi daga biranen Beijing, da Urumqi, da Lanzhou, da Yinchuan, da Xining, da Kunming. Da farko, za su yi ziyara da sauran ayyukan ibada a birnin Madina a tsawon kwanaki biyar, sa'an nan za su tashi zuwa Makka don sauke farali.
Kungiyar mabiya addinin Islama ta kasar Sin, ta zabo ma'aikata sama da sittin, wadanda za su samar da hidimomi daban-daban ga maniyyatan aikin hajjin na bana, wadanda suka kunshi ayyukan ibada, da kiwon lafiya, da tsaro, da abinci da gidajen kwana da sauransu, ta yadda maniyyatan za su sauke faralinsu lami lafiya kuma ba tare da fuskantar wata matsala ba.(Murtala Zhang)