in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi bikin faretin murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA
2017-07-30 15:31:35 cri

Ranar 1 ga watan Agusta na shekarar bana, rana ce ta cika shekaru 90 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin ta PLA, domin taya murna ta wannan muhimmiyar rana, da karfe 9 na safiyar yau, an yi bikin fareti a sansanin horaswa dake garin Zhurihe na jihar Mongoliya ta gida. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi.

Yanzu ga cikakken rahoton da Maryam ta hada mana:

Wannan shi ne karo na farko da aka yi faretin yake-yake a sarari domin taya murnar ranar kafuwar PLA bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, kana karo na farko da aka yi faretin tun bayan da aka fara aiwatar da kwaskwarima kan tsarin kiyaye tsaron kasa, da kuma rundunar sojojin kasar ta Sin. Gaba daya akwai sojoji kimanin dubu 12 da suka halarci bikin, yayin da jiragen saman soja sama da dari daya, da kuma kayayyakin soja sama da dari shida.

Bayan faretin, sojojin sun taru a gaban babban dandalin duba fareti domin sauraron muhimmin jawabi na shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, inda ya yi tunawa kan muhimman ci gaban da rundunar 'yantar da jama'ar kasa ta Sin ta samu cikin wadannan shekaru 90 da suka gabata, yayin da ba da sabon umurni gare ta domin karfafa kwarewarta cikin sabon zamani.

"Jin dadin zaman lafiya shi ne babban alheri ga al'ummomin kasa ta Sin, kiyaye zaman lafiya shi ne nauyin dake wuyan rundunar sojojin kasar. A halin yanzu, ana fama da rikice-rikice a kasashen duniya, ya kamata a dukufa wajen kiyaye zama lafiyar kasa da kasa. Shi ya sa, ana bukatar ginawar rundunar sojoji mai karfi a kasar Sin domin cimma burinmu na samun farfadowar kasa baki daya. Haka zalika, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta ci gaba da karfafa ayyukan rundunar sojojin kasar bisa hanyoyin da za su dace da halin musamman na kasar Sin, domin cimma burinta na ginawar rundunar PLA wadda za ta kasance gaba cikin kasashen duniya."

Bugu da kari, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da sabon umurni ga dukkan sojojin rundunar PLA, inda ya bukaci dukkan sojojin runduanr PLA da su nuna goyon baya ga jagorancin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi musu ba tare da nuna shakku ko kadan ba, da kuma bauta wa al'ummomin kasar Sin yadda ya kamata, yayin da karfafa kwarewarsu ta yin yake-yake ba tare da kassala ba. Haka kuma, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen kyautata kwarewar sojojin kasar wajen kiyaye tsaron kasa ta hanyoyin da suka hada da, tsara shirin siyasa wajen kafuwar rundunar sojojin kasar, karfafa karfin rundunar sojojin kasar ta hanyar yin kwaskwarima, kyautata harkokin soja da abin ya shafa ta hanyar kimiyya da fasaha, da kuma gudanar da harkokin soja bisa dokokin kasar.

Shugaba Xi yana mai cewa:

"Ina da imanin cewa, tabbas ne rundunar PLA na kasar Sin za ta iya cimma nasarar yaki da duk wanda yake da aniyar keta ikon kasar Sin, kuma, babu shakka, tana da karfin kiyaye mulkin kai da tsaron kasa, da kuma ikon kasar wajen neman ci gaba. Tabbas ne za a iya bude wani sabon shafi ta fuskar karfafa karfin rundunar sojojin kasar, ta yadda za ta ba da gudummawa matuka wajen cimma burin kasar Sin na neman farfadowar kasa da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya".

Bayan shugaba Xi Jinping ya kammala jawabinsa, dukkan sojojin sun yi tafi ba tsayawa a dandalin bikin fareti.

Kasashen duniya da dama su kan yi bikin fareti a yayin muhimmiyar rana, a yau Lahadi, kakakin ma'aikatar tsaron kasa ya bayyana cewa, an tsara wannan bikin fareti bisa jadawalin horaswa na rundunar PLA, babu la'akari da shi da yanayin yankin iyakar kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China