in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya yi kira da a yi hadin gwiwa don yaki da kwararowar Hamada
2017-07-30 10:36:35 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kiran a yi hadin gwiwa na kut-da-kut a tsakanin kasashen duniya da shiyya shiyya wanda ya kunshi yankunan hanyar ziri daya hanya daya don yaki da kwararowar Hamada.

Ya bayyana hakan ne a cikin sakon fatan alheri da ya aikewa taron dandalin Kubuqi na kasa da kasa kan yaki da kwararowar Hamada wanda aka bude shi a ranar Asabar a Kubuqi dake arewacin yankin Mongoliya ta gida ta kasar Sin mai cin gashin kai.

Xi ya ce, kwararowar Hamada babban kalubale ne dake addabar duniya, ya kara da cewa daukar matakan kariya daga fuskantar kwararowar Hamada al'amari ne da zai amfani al'ummar wannan zamani da al'ummomi da za su zo a nan gaba.

Ya ce kasar Sin a ko da yaushe tana ba da muhimmanci wajen yaki da kwararowar Hamada kuma ta cimma nasarori masu yawan gaske.

Taken taron kolin na wannan shekara shi ne, "Samar da koren muhalli a kan hanyar ziri daya, da kula da tattalin arzikin muhallin halittu," Xi ya ce, abu ne mai matukar muhimmanci a hada karfi da karfe domin yin riga kafi da kuma yaki da kwararowar hamada a tsakanin kasashen duniya da shiyyoyin dake kan hanyar ziri daya da hanya daya.

Kana ya bukaci wakilan kasashen dake halartar taron da su yi amfani da hikimominsu kuma su bada gudunmawa wajen samar da koren muhallai a kan hanyar ziri daya da hanya daya da inganta kula da muhallin halittu a duniya baki daya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China