in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin haraji na kasashen BRICS sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta hadin kai
2017-07-28 11:04:17 cri

Hukumomin kula da haraji na mambobin kungiyar kasashe masu samun saurin ci gaban tattalin arziki wato BRICS, sun rattaba hannu kan wani daftari dake da nufin samar da hadin kai tsakaninsu ta fuskar ayyukansu.

Yarjajeniyar fahimtar juna kan harkokin harajin da aka rattabawa hannu yayin taro na 5 na shugabannin hukumomin haraji na kasashen, ita ce irinta ta farko da kungiyar ta tsara don shigar da batun haraji zuwa matakin hukumomin kasashe mambobinta.

Yayin taron, hukumomin sun amince su hada hannu wajen musayar bayanai da inganta tsarin tuntuba da bunkasa harkokin karbar haraji tare da tsara hanyoyin samar dabarun kula da karbar haraji.

Taron ya zo ne gabanin babban taron kungiyar na bana da za a yi a lardin Fujian daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Satumba.

Kasashen BRICS da suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da Sin da Afrika ta kudu, muhalli ne ga kashi 42 na al'ummar duniya.

Jimilar kason su na tattalin arzikin duniya ya tashi daga kashi 12 zuwa 23 cikin shekaru goma da suka gabata, yayin da suke ba da gudunmuwar sama da rabin ci gaban duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China